Fitaccen mai bada umarni a fina finan Hausa na Kannywood, Aminu S Bono ya bayyana damuwarsa da yadda ake yawan fito da manyan jarumai mata a kusan kowanni Fim, inda ya bayyana hakan a matsayin wata babbar kalubale.
Daraktan ya koka kan karancin sabbin jarumai Mata, inda yace hakan ne ya sanya tsofaffin jarumai irinsu, Jamila Nagudu, Fati Washa, Aisha Tsamiya, Hadiza Gabon da sauransu yin kane kane a masana’antar Kannywood.
Bono ya cigaba da cewa kamata ya yi a ce tsofaffin jaruman sun koma fitowa a matsayin iyaye saboda girma ya fara kamasu, amma saboda karancin sabbin jini ya sa duk an bi an raja’a akansu, sai dai yace sun fara kulla kulalliyar yadda zasu yi musu juyin mulki da sabbin taurari.
“A yanzu mun fara fito da sabbin jarumai Mata, da suka hada da Zee Preety, Amal Umar, Bilkisu Shema, Zulaihat Ibrahim, Maryam Yahaya da sauransu, ta hanyar fito dasu a bidiyon wakoki da ba na fim ba. Inji su
Da yake amsa tambayar ko rashin ganinsu Jamila Nagudu a Fim zai kawo nakasu ga amsuwar Fim, sai yace “Su ma kafin su zo, su Fati Muhammad ne ke haskawa, kuma zuwan nasu ya kawo musu cigaba”.
Ya cigaba da cewa yanzu an wuce lokacin da mata masu zaman kansu ke shigowa Fim, don kuwa a yanzu a cikin Mata goma da zasu yi rajistan fara Fim, za’a iya samun bakwai daga cikinsu masu digiri ne ko kuma suna cikin karatun digirin.