Jaruman Kannywood 6 Da Ska Shiga Dakin Aure A Bana


Wasu daga cikin manyan jarumai dake nishadantar damu sun shiga sahun sauran abokan aiki su, sun shiga dakin aure.

Ga wasu jaruma daga cikin jarumai da suka yi aure bana:
1. Abida Muhammed
Tsohuwar fitatcciyar jarumar Kannywood, ta sake aure bayan mutuwar tsohon mijinta. An daura auren ta da sabon angonta Mustapha Abubakar, ne ranar juma'a 26 ga watan janairu na 2018 a nan garin Kano.

2. Sa'idu Muhammed
Shima shaharraren jarumin fina-finan turanci wanda aka fi sani da funky mallam, ya kara aure bayan rabuwar shi da tsohuwar matar shi. Auren sa da tsohuwar matar shi, sun samu da namiji.
3. Sadiya Adam
Bana dai auren wannan jarumar yana daya daga cikin bukukuwan da suka yi yawo a kafafen sada zumunta. Bikin aurenta ya samu halarta daga wasu daga cikin manyan abokan sana'ar ta na Kannywood. An dauren auren ta da angonta  Alhaji Sanusi Ahmad ranar lahadi 1 ga watan Afrilu a garin Zaria.

4. Sadiya Kabala
An daura auren jarumar Kannywood da angonta,Ahmad Isa ranar asabar 14 ga watan afrilu a masallacin Al-mannar dake nan garin Kaduna.
5. Aminu Dagash
Shima jarumi ya shiga sahun sauran abokan aikin sa na masana'antar nishadantarwa. An daura auren sa da amaryar shi ranar 31 ga watan Maris.

6. Mc Ibrahim Sharukan
Duk da cewa an sa rana amma ba'a daura ba, bari mu kara da auren shahararren jarumi kuma babbar mai gudanar da shirye-shiryen biki. Za'a daura auren Mc Ibrahim Sharukan da amaryar shi, Halima Shehu Usman, ranar 5 ga watan mayu.

Post a Comment

0 Comments