Tauraruwar fim Hadiza Aliyu Gabon ta fito da zafi-zafin ta wajen saka wando daya da wadanda kudin ta ke hannun su.


Duba da sakonnin da ta fitar, duk wani mai rike da kudin ta ya shirya fuskantar fushin ta idan baiyi gaggawa wajen biyan bashin.

Hadiza Gabon ta kai makura kuma kamar yadda ta sanar bata son jin wani labari, kudinta kawai take bukata kuma idan ba'ayi hakan ba zata fallasa sunayen masu.



A cikin jerin sakonnin da ta wallafa a shafin ta daya bayan daya, jarumar tace bata son wadanda ke bin ta bashi su kira ta ko su tura mata sakon. Iya sakon da take son ta gani daga gare su shine alamar an tura mata kudinta.

"Kar mutum yace zai mun Dm da sunan na daina" ta rubuta bayan ta wallafa cewa "An dinga biyan bashi. Wallahi zan kira sunayen ku".

Cikin kudin ta dake hannun jama'a akwai miliyan N2.8 da dubu N350 da dubu 75 da dubu N30.

kamar yadda ta sanar, ciki akwai kudin aikin da tayi ba gama biyanta da kuma kasuwanci da tayi shima ba'a biya ta kudin ta ba.

Duk dai tayi masu kudin goro, tace wannan karon batun "yin hakuri".


Da yawo daga cikin masu bibiyan ta kafafen sada zumunta sun goyi bayan matakin da ta dauka kuma sun koka kan yadda mutane ke cin bashi ba tare da nuna alamar biya.

Ga wanda tame son ta isar ma sakon, wannan ba abun wasa bane kuma da alama matakin karshe da jarumar zata dauka ba zai yi dadi ba.