Ganawar da Ali Nuhu da wasu taurarin fina-finan Hausa suka yi da kakakin mjalaisar dattijai, Bukola Saraki ta jawo cece-kuce tsakanin wasu manyan jaruman masana'antar ta fina-finan Hausa, inda wasu ke ganin wadanda suka wakilci masana'antar, musamman ta bangaren mata ba wasu fitattun jarumai bane.

Manyan jarumai biyu mata sun kasa hadiye abin inda suka fito suka nuna rashin jin dadinsu a fili.

Rahama Sadau ta yi magana me kama da shagube a dandalinta na sada zumunta inda ta bayyana cewa, Kakakin majalisar tarayya, Bukola Sataki ya gana da sarkin mu da kuma wasu daga masana'antar Kannywood, da kuma matan dake jan ragamar masana'antar fina-finan Hausa.




Nafisa Abdullahi ta mayar da martani akan wannan batu inda tace:

Wadannan hotunan sun nuna icewa da wuya masana'antar fim din Hausa takai matakin(cigaba) daya kamata takai, ni dai ban san wadannan matan ba amma gasu nan(da su aka je).



Nafisa ta kara da cewa, babu ta yanda zamu ci gaba idan babu hadin kai da gaskiya a tsakaninmu, wannan abin kunyane, lallai kam ai sai mata masu jan ragama. 

Raham ta kara da cewa, gaskiya nayi tsammanin ganin Jamila, Nafisa , A'isha ko hadiza a cikin wannan tawagar, amma ni dake mun san yanda masana'antar ke gudana, watakila kamun kafarsune yasa akaje dasu, kinga kuwa doke asa su wakilcemu.


Ali Nuhu shima ya mayar da amsa ga Rahama inda yace, 'yar uwa, ba zaki kashe ni ba, cikin barkanci.



A cikin maza dai ba'a samu wanda ya fito fili ya soki wannan lamariba, sai ma Adam A. Zango daya saka labarin,alamar yana murna dashi kuma masoyanshi sun yaba mishi akan hakan.

Source: HutuDole.