Na Yi Da Na Sanin Auren Sani Mai Iska – Jaruma Fati Muh’d


Tsohuwar fitacciyar  jarumar nan ta masana’antar Kannywood, Fati Muhammad, ta bayyana auren jarumi Sani Musa Mai Iska a matsayin babbar nadamar ta a rayuwa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da jaridar Blue Print inda ta bayyana cewa ta amince da cewa kowa na da jarabawar da Allah ya ke yi masa sannan kuma tace ita dai jarabawar ta ta fannin aure ta ke.

jarumar ta kara nanata maganarta da tayi a baya inda tace ba fa zata kara auren dan fim ba koma waye.

Idan za ku iya tunawa,Fati Muhammad, ita ce ta fito a cikin tsohon fim din nan na Sangaya tare da jarumi Ali Nuhu, a matsayin Zubain, wannan fim din nan ya fito da ita.

Madogara: Fimhausa

Post a Comment

0 Comments