Adamu Zango ya tayar da kura a Instagram


Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa, Adamu Abdullahi Zango ya tayar da kura bayan ya sanya wadansu hotuna biyu a shafinsa na Instagram.
Jarumin wanda ake kira da Fresh Prince ya sanya hoto na farko hannunsa a kan kafadar wata budurwa da ya kira ta da suna Hanaan.
A hoton jarumin da budurwar suna dariyar farin ciki, sannan a karkashin hoton jarumin ya rubuta kamar haka: “Yawancin mutane suna so ku yi tafiya da su a cikin mota kirar Limo, amma abin da kake so shi ne ka samu wanda zai yi tafiya da kai a mota bas idan Limo din ta baci. Na yi farin ciki da ganin ki @hanaan, ’yar uwata.”
Hoton ya tayar da kura, inda hakan ya sanya jarumin ya kara sanya wani hoto mai dauke da mutane hudu.
A hoto na biyun, jarumin ya dora hannuwansa biyu a kan kafadun wadansu mata biyu, yayin da wani matashi mai gemu yake daga farko ta bangaren dama a hoton. A hoton dukkansu suna dariya.
Hakan ya sa wani daga cikin mabayan jarumin a Instagram mai suna Hamid Ibrahim cewa, “Wannan ba dabi’a mai kyau ba ce, a dai rika yi ana tunawa da mutuwa.”
Ita kuwa Khadijat Arabi cewa ta yi sai masu hassada da Zango su kashe kansu, amma babu yadda za su yi da Zango.
“Sai dai masu hassada ku kashe kanku, amma Zango ya yi gaba.” Inji ta.
Samira Hassan kuwa cewa ta yi, budurwar da jarumin ya dora hannu a kafadarta yayin daukar hoton, to ’yar uwarsa ce ta jini, don haka babu wani laifi, ko abin cece-kuce da za a ce jarumin ya jawo.
Shi kuwa Ahmed Isa cewa ya yi Zango abin koyi ne ga miliyoyin jama’a, don haka bai kamata ya rika sanya irin wadannan hotuna ba.
Ya ce, “Zango kai babban jarumi ne, wanda miliyoyin jama’a suke koyi da kai, don haka bai kamata ka sanya irin wadannan hotuna ba.”
Haka ne ya sanya Adam A. Zango yin karin bayani, inda ya ce wacce ya dauki hoton da ita kanwarsa ce, kuma babu laifi don ya taba kanwarsa, al’amarin da ya sanya mutane suka sake yi masa caa! Kasuwar kuda.
Ibrahim Idris ya ce, bai gamsu da bayanin da jarumin ya yi ba, inda ya ba shi shawara ko da zai dauki hotuna da ’yan uwansa, to ba lallai sai ya dafa su ko ya rungume su ba.
“Koda ’yan uwansa ne bai kamata ya dafa su ba, bai kamata ya rungume su ba, kowa ya san yadda akuyar ’yan fim ta yi kuka, ana yi musu kudin goro wajen kiransu ’yan iska, don haka sai ya bar halal don kunya. Ma’ana bai san adadin wuraren da hotunan za su zaga ba, ba kuma kowa ne zai gane cewa ’yan uwansa ba ne, wadansu za su yi amfani da hotunan wajen yada sharri.
“Su rika cewa ga abin da ’yan fim din Hausa suke yi, kamar yadda aka rika yada na Nafisa Abdullahi da Zainab Indomie da Ibrahim Maishinku da sauransu, don haka ina ganin rashin sanya hotunan shi ne mafi alheri a kan sanya shi.” Inji Idris.
Amina A. Baba a lokacin da take tofa albarkacin bakinta cewa ta yi ko da jarumin zai sanya hotunan da suka shafi ’yan uwansa ba lallai ne sai ya dafa su ba.
“Idan har ya zama dole sai jarumin ya sanya hotunansa tare da ’yan uwansa, to bai zama dole sai ya dafa su ba, za su tsaya ko su zauna a dauki hoton ba tare da ya dafa su ba, hakan kwata-kwata bai dace ba, kuma ya kamata Zango ya sani shi fa ba yaro ba ne, kuma ya san dole jama’a za su caccake shi amma ya sanya, inda hakan yake nuna cewa da gangan ya yi,” Inji ta.
Hakan ne ya sa daga baya jarumin ya boye maganganun mutane dangane da hotunan, duk da cewa har zuwa lokacin da aka kammala rubuta wannan rahoto bai cire hotunan ba.

Post a Comment

0 Comments