Sabuwar Manhaja Da Yara Zasu Iya Koyar Da Kansu, Batare Da Zuwa Makaranta Ba


Wai kuwa yara da basu taba zuwa makaranta ba, na iya koyar da kansu yadda ake rubutu da karatu, daga kawai sun samu na’urar kwamfuta? Wata tambaya da wata kungiya mai yunkurin ilmantar da duniya tayi ke nan.
Kungiyar ‘Global Learning XPRIZE’ ta ware makudan kudade da suka kai kimanin dallar Amurka milliyan goma sha biyar $15M, don cinma wannan burin. Daya daga cikin daraktocin kungiyar Mr. Matt Keller, yake cewar, wannan kamar abu ne mai wuyar yuwuwa.
Kana shawarar na iya zama kamar hauka, domin kuwa ance yaro ya koyar da kanshi da kanshi, daga amfani da kwamfuta, an dai bama kungiyar kwantirakin fitowa da wata sabuwar manhaja, da yara wadanda basu samu damar zuwa makaranta ba, zasu iya amfani da ita wajen koyar da kansu da kansu.
A kididdigar tsangayar lissafi ta hukumar kula da kayan tarihi na majalisar dinkin duniya UNESCO, ta tabbatar da cewar, akwai kimanin yara sama da milliyyan dari biyu da sittin da uku, a duniya da basa zuwa makaranta.
Hakan yasa suke ganin akwai bukatar samar da wannan manhajar, don a ilmantar da kowa, ya zuwa yanzu dai an samu wasu kamfanoni da zasu gudanar da aikin, yanzu haka ma ana sa ran a watan Nuwamba za’a fara gwajin wannan manhajar.

Post a Comment

0 Comments