Yadda Tauraruwan Shahararren Mawaki Umar M. ShareeF Ke Haskawa


 Idan ana maganar jarumi kuma fasihin matashi mai saukin kai, tabbas ba za gushe ba sai an ambaci Umar M. Shareef, domin manazarta da marubuta harkokin wakoki da fina finai, sun bayyana cewa, tun bayan  kafuwar masana'artar shirya finai finai, baya ga Margayi Ahmed S. Nuhu, har yau ba a sami matashin da ya kai Umar M. Sharif saukin kai da yin  biyayya ga  na gaba da shi ba.



Wannan yana daya daga cikin dalilin da yasa Jarumin Sarkin Kannywood Ali Nuhu, a karon farko ya shirya masa wani shaharren film mai suna MANSOOR. Film da masana sukayi itikafin cewa ba'a taba yin wani film mai farin jini da saurin karbuwa a zukatan masoya kallon fina finai  irin wannan film din ba, domin mana zarta  harkokin shirya fina finai sun bayyana cewa, tun daga ranar da aka fara haska film din MANSOOR a gidajen kallo na Silma, sama da mutum miliyan biyar ne ke bibiyar wannan film din, kuma duk ba domin komai ba, sai domin irin yadda film ya yi tasiri  sosai da ma'ana.

A gefe daya kuma, wasu na kallon karbuwar film din MANSOOR bai rasa nasaba da yadda masoyan  Umar M. Sharif suka kagara suyi ido hudu da jarumin da ya dade yasa sanyaya masu rai ta bangaren wakokinsa mai dauke da duk wani launin saukin SO irin na ma abota bege.



Al'umma na bayyana Umar M. Sharif a matsayin jarumin da bai dauki girman kai ya daura ma kansa ba, domin idan ka cire lokacin aiki, duk sauran lokutan Umar M. Sharif na yinsu ne cikin 'yan uwa masoya da kuma abokan arziki, wanda hakan ke nuna cewa lalle Umar mutum ne mai saukin kai da kuma girmama na gaba da shi.


Masana harkokin fasahar wakokin hausa, sun bayyana cewa, har yau babu wani matashin mawaki da har gobe tauraronsa ke haskawa a kullum tamkar Umar M. Shareef. Domin a sanadiyar irin wannan daukaka ne, ya sanya shaharren mawakin kudancin kasar nan Sele BoBo ya gayyaci Umar M. Sharif har Birnin Lagos domin daukar gammayar wakoki a tare, wanda kusan wannan wakoki da sukayi a tare ya shahara sosai da sosai, domin duk lungu da sakon ciki da wajen kasar nan ana sauraren wannan wakoki na Umar M. Shareef Da Sele BoBo.



A cikin zantawarsa da manema labarai a kaduna, Umar M. Sharif ya bayyana irin daukakar da yake samu a matsayin wani hikima daga Allah. Sannan ya bayyana cewa har abada ba zai taba mantawa da irin gudumuwar da Jarumi Ali Nuhu yake bashi ba, bawai kawai akan film din MANSOOR ba, a a, akan duk harkokin sa na yau da kullum, domin a cewarsa, Ali Nuhu ya gama masa komai a rayuwa.

Umar M Shareef ya kuma bayyana irin yadda tun farko ya samu goyon baya daga wajen Mahaifa da 'yan uwansa, domin a cewarsa, film da waka ya zama jinin jikinsa, ko ba domin komai ba, sai yadda gidansu ya ke alfahari da jarumai masu yawa wanda ake alfahari da su a farfajiyar masana'artar Kannywood.

Daga karshe Umar M. Shareef ya gode ma dumbin masoyan sa dake bibiyar duk harkokin lamarinsa, wanda a cewarsa, da bazar masoyan sa yake rawa, kuma da izinin Allah ba zai basu kunya ba, domin zai ci gaba da nishadantar dasu fiye da yadda suke zato.

Post a Comment

0 Comments