Wata Mata Ta Sayar Da Jaririnta Ta Sayi Babur (Mashin)

Wata matashiya, yar shekara 24 da haihuwa ta sayar da sayar da jinjirin da ta tsuguna ta haifa (dan wata biyu da haihuwa) akan kudi Naira dubu 250, inda ta yi amfani da wani bangare na wannan kudi wajen sayen mashin (babur)

Wannan matashiya mai suna Oluchi Emeobi, ‘yar asalin karamar hukumar Nnewi ce da ke jihar Anambra a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

Kwamishina ‘yan sandan jihar Anambra, Umar Garba ya tabbatar mana da cewa Oluchi ta shiga wannan mummunar harkalla na cefanar da danta dan kimanin watanni biyu da haihuwa kuma ta yi amfani da wani bangare na kudin ta sayi mashi don ragewa kanta wahalar zirga-zirga a kafa

Sai dai tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta cafke Oluchi tare da karbe babur din da ta saya da kudin jariri

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar mana da cewa Oluchi ta yi wannan harkalla ne da taimakon wata Nchedochi Richard, mai shekaru 26 da haihuwa wanda ke zaune a gida daya da Oluchi
 Da jin cewa ‘yan sanda sun yi ram da Oluchi, sai Nchedochi da aka fi sani da First Lady ta ranta a na kare ta yi kuma layar zana domin har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, ba a yi nasarar samunta ba

A yayin da kwamishinan ‘yan sanda ke bayyana ‘yan jarida wannan lamari, ya ce “Oluchi ta kai rahoto wajen ‘yan sanda cewa, ta bar jaririn nata a wajen wace mace da ba ta sani ba, amma kafin ta je ta dawo, matar ta gudu da jaririn”

Bayan ‘yan sanda sun tsananta bincike ne sai suka gano cewa Oluchi ce da kanta ta cefanar da jaririn nata kuma har an samu kudi Naira Dubu Dari Biyu Da Hamsin da kuma babur a wajenta, wanda bincike ya nuna cewa daga cikin kudin harkalla ne suka fito

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Anambra, Umar Garba, ya tabbatar mana da cewa har yanzu suna ci gaba da yin bincike don gano wanda ya sayi jaririn da kuma inda jaririn yake

Creadited: Arewarmu.Com

Post a Comment

0 Comments