Sabon tsari don ‘yan bana bakwai, kamfanin yada zumunta na facebook, na shirin kaddamar da sabon tsari a shafin su na facebook Instagram, wanda za’a iya amfani da manhajar, wajen makala wasu abubuwan ban dariya, tsoro, abubuwan ban sha’awa da dai makamantan hakan.
Wannan sabon tsarin zai dinga tsame fuskar mutun, da kuma ba mutun damar saka duk wata sura da yake sha’awar sawa, don mutane da yake ganawa da su a bidiyon kai tsaye suga abun da ya saka.
Haka mutun na iya saka wasu rubuce-rubuce kamar na lissafi, da duk wani abu da yake iya nuna abun sha’awa ga mutun, tsarin kuma zai ba mutane damar kallon bidiyo ta baya-da-baya, wanda mutun zai ga yadda aka dauki bidiyon kamin isa karshen bidiyon.
Kamfanin dai na facebook, sun fito da wannan sabon tsarin ne, don yima abokan hamayyar su 'snapchat' zarra, duk dai da cewar mutane na ganin cewa,r kamfanin na facebook suna kwaikwayon tsarin kamfanin snapchat.
Kamfanin na snapchat sune asalin makirkira tsarin ‘Stories’ wanda shafin na facebook suma suka kwaikwaya. Kimanin mutane sama da milliyan 200 ne suke amfani da wannan tsarin a kowace rana a fadin duniya.
0 Comments