Me Zai Faru Da Kai Idan Matarka Ta Bata Maka Rai?



Masu karatu da membobin wannan Shafi Hausamini mai albarka, a yau na dan tsakuro muku wata tsaraba daga shafin ‘Zauren Fikhu’ a dandalin ‘Facebook’ domin amfaninmu baki daya.
Zauren ya shahara, inda malamai ke bayanai da dama da suka hada da dukkanin al’amuran rayuwa a addinance. Misali, ko ka san abin da zai same ka idan matarka ta bata maka rai? Maza karanta wannan ka sha mamaki:
Ko kasan cewa duk lokacin da matarka ta ‘bata maka rai in dai kayi hakuri domin Allah, akwai wasu alkhairai da zasu sameka kamar haka:
  1. Idan Matarka ta bata maka rai, nan take matanka na gidan Aljannah su mayar da martani a gare ta (sai dai ba za ku ji ba). Ta ce: “Ke da kike ta bata masa rai, ai ya kusa dawowa zuwa gare mu, inda zai dauwama cikin farin ciki.”
  2. In har ka yi hakuri domin Allah sai Allah ya rubuta maka lada mai dimbin yawa, ba tare da lissafawa ba. Kamar yadda Ya ce, “Ana bama masu hakuri ne ladansu ba tare da lissafi ba.”
  3. Idan ka yi hakuri domin Allah, to nan take Allah zai zama naka. Wato Allah yana tare da masu hakuri.
  4. Idan ka yi addu’a, Allah zai amsa maka a lokacin. Domin Allah yana saurin amsa addu’ar wanda aka zalunta. (Ka ga za ka iya rokon Allah ya canza halayenta, ko kuma ya canza maka wacce tafi-ta alkhairi).
  5. Allah zai daukaka darajarka a duniya da lahira saboda albarkacin hakurinka. (Hakuri, afuwa, ba su kara maka komai sai dai girma a wajen Allah).
  6. Ubangiji zai kara maka yawan matan da za a ba ka a gidan Aljannah. Tun da za ka samu karin daraja a Aljannar, kenan za ka samu karuwar ni’imah a cikinta
  7. A ranar lahira Allah zai kira ka a gaban dukkan halittu, sannan ya ce maka: “Ka shiga Aljannah ta duk kofar da kake so.” (Haka Manzon Allah (saw) ya ce: “Duk wanda ya danne fushi, alhali yana da ikon zartar da shi, Allah zai kira shi a ranar Alkiyamah a gaban dukkan halittu, sannan ya ce masa ‘Shiga Aljannah ta duk kofar da kake so,’”).
Manzo (saw) ya kara da cewa, “Ku rika yin hakuri da mata.” Ya san cewa su mata wasu irin halittu ne. Ba za ka rayu cikakkiyar rayuwa ba dole sai da su. Idan kuma kana tare da su sai sun rika muzguna maka. Mafi yawansu akwai su da rashin godiyar Allah, rainin wayo, rainin hankali, ga taurin kai, ga tsananin kishi, ga Hayaniya, da sauransu.

Post a Comment

0 Comments