Labarin Maryam Sanda Ya Janyo Gobara A Kannywood


Babban daraktan hukumar tace finafinai da dab’i na jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba Afakallahu, ya bayyana cewa, ba a fahimce shi ba kan batun takardar da ya aike wa furodusan wani sabon fim, Malam Abdul Amart, wacce a cikin wasikar a ka bayar rahoton cewa ya soki lamirin masu shirya finafinan Hausa da alhakin janyo wa ma’aurata su na kashe rayuka.

Malam Afakallahu ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da editanmu a karshen makon nan ta wayar tarho, inda ya kara da cewa, korafe-korafen da hukumarsa ke samu daga al’umma ne su ka sanya ya dauki matakin kin amincewa da tallen wani fim din na Furodusa Abdul Amart har sai an duba shi gabadaya, domin hukumar na zargin ya yi kama da labarin Maryam Sanda, wacce a yanzu ta ke gaban kotu a babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja, bisa zargin kashe mijinta, Bilyaminu Halliru, dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

A daya bangaren kuma, hadaddiyar kungiyar masu shirya finafinai, MOPPAN, ta tuntubi wakilinmu, inda ta shaida ma sa cewa, za ta maka hukumar Malam Afakallahu a gaban kuliya manta sabo, domin ba kage a ka yi ma sa ba, saboda kungiyar ta na rike da wasikar da su ke zargin an bata mu su suna bisa danganta su da kashe-kashe da mata ke yi a gidajen mazajensu.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin sakataren MOPPAN reshen jihar Kano, Malam Salisu Muhammad Officer.

Amma Afakallahu, wanda ya nanata cewa hukumarsa ta na da kyakkyawar alaka da masu shirin fim a jihar, ya kara da cewa, “wannan fim ba shakka an kawo shi ga hukuma, amma saboda korafi da mu ke samu daga al’umma cewa a na fito da wuka a na fito da makamai su na zama maimakon su koyar sai ya zamana wadannan finafinai su na karantar da wannan abubuwan ne (na kashe-kashe), shi ne hukuma ta dauki mataki.
Afakallahu ya kara da cewa, “a bisa tallen fim din da a ka kawo, amma ba mu tabbatar ba, (fim din) ya na kamanceceniya da shi wannan (labari) na Maryam Sanda din.

Shi ya sa a ka ce a kawo fim din a kalla kacokam, domin a kiyaye hakkin kowane mutum, sannan kuma a ga cewa, abinda a ke son a yi, shin a na so a yi ne don gyara ko yada abinda a ka yi daidai ne ko ba daidai ba ne?
“Sai mu ka ce, to shi mai fim ya kawo ma na fim din gabadaya a kalla. Idan mun ga cewa babu
matsala wacce za ta kawo lalacewar al’umma da a ke zargi, mu bar shi da fim dinsa ya je ya saka. 

To, daga nan sai ya fita ya je ya sake shi a Youtube da sauran ‘social media’, wadanda mu ba mu da hurumi a wurin.
Shi ya sa mu ka rubuta takarda ga kungiyoyin masu finafinai da kungiyoyin dukkannin masu ruwa da tsaki, domin kada wani ya je ya dauki wannan talle ya saka shi a fim, kuma ya je a ce ba za a duba fim dinsa ba, shi ya zama an ja ma sa asara, amma ita hukuma ba ta ce ba za ta duba fim ba.”
Malam Isma’il Na’abba ya kara da cewa, ba kwaikwayar labarin da ta faru a zahiri ba ne, illa dai a yi labarin da ba zai zama cutuwa ga al’umma ba, domin a cewarsa wani labarin fim din zai iya zama guba ga ita al’ummar.
Amma yayin da ya ke mayar da martani kan ko da gaske ne Afakallahu ya yi wancan furuci na zargin ’yan fim kashe-kashen ma’aurata a waccan wasika, Malam Salisu Officer, ya ce, “gaskiya ne ya yi furucin haka. Abinda ya sa shi ne, akwai takarda da ya aikawa dukkanin kungiyoyin fim da rukunoninsu a kan wata tirela ta wani mai shirya finafinai, Andul Amart, saboda ya ga tallen fim din a Youtube, sai ya aika cewa ba zai duba ba tirelar ba, domin mu sani cewa sun yanke shawarar ba za su duba finafinai masu wannan tirela da Abdul Amart ya kai mu su ba.

“A cikin wasikar tasa (Afakallahu) a sakin layi na biyu ya fada cewa, dalilinsa na yin haka shi ne mu na fitar da finafinai da yawan gaske (wato rampant), wadanda kallon wadannan finafinai ya jawo yara matasa su na daukar dabi’un da su ka gani na makamai na kisa a finafinanmu da kuma ma’aurata (wanda) ya jawo rasa rayukan wasu wadanda su ke da auratayya.

“Wannan shi ne abinda ya fada, ya kuma nanata a cikinta (wasikar) a sakin layi na uku. Wannan ba wai kage a ka yi ma sa ba. Takardar ta na hannun dukkan kungiyoyi da kuma rukunonin shirya finafinai da ya aikowa a kan wannan tirela da shi Abdul Amart.”

Daga nan sai Officer ya bayyana matakin da MOPPAN ke shirin dauka kan batun, inda ya ce, “mun kalli takardar nan a matsayin bata suna, a matsayin kuma wani abu da zai jawo ma na bakin jini a cikin al’umma,” ya na mai cigaba da cewa sun yanke shawarar, “a rubuta ma sa (shi Afakallahu) takarda a kan cewa mu ba ma daya daga cikin wannan zargin da ya yi, sannan kuma ba shi da hurumi a kan finafinai da su ke intanet, amma huruminsa ne ya ki duba tirela ko ya duba, sannan mu saurari amsarsa.

“Idan bai ba mu amsa gamsasshiya a kan wannan takardar kage ko sharri da ya yiwa masana’antar shirya finafinai ba, za mu shigar da shi kotu, domin a bi ma na kadin abinda ya yi.”

Daga: Leadership Ayau

Post a Comment

0 Comments