Jerin Jaruman Da Suka Lashe Kyautar KannyWood AMMA Award Na Bana



Taurarin fina-finan Hausa da damane suka samu kyautukan karramawa na masu karrama mawaka da 'yan Fim na Hausa da ake kira da AMMA, Ali Nuhu ya samu kyautar me bayar da umarni na shekara saboda fin din Mansoor da ya bayar da umarnin yinshi.

Haka ma danshi, Ahmad ya samu kyautar zama tauraro tsakanin yara dake fim.

Tauraron mawaki kuma sabon jarumi, Umar M. Shareef shima ya samu kyautar tauraron jarumi tsakanin jarumai masu tasowa.

Sai kuma Amal Umar da ta samu kyautar jaruma mace tsakanin jarumai masu tasowa.

Halima Atete ce ta amshi kyautar jarumar jarumai mata masu fitowa taurarin fim.

Sai kuma Hafsat Idris da ta samu kyautar fuskar shekara.

Dan gidan T. Y Shaban, Sani, shima ya samu kyautar karramawa.

Sai kuma sabuwar jaruma, Maryam Abubakar wadda itama ta samu kyautar karramawa ta farko.

Hamisu Lamido Iyantama, Ado Ahmad Gidan Dabino, Hafizu Bello duk sun samu kyautukan karramawa.

Da su da sauran dukkan jaruman da suka samu kyautukan karramawa, muna tayasu murna da fatan Allah ya kara daukaka.








Post a Comment

0 Comments