Fadan Ali Nuhu da Adam Zango ya 'raba kan Kannywood'


Za a iya cewa babu wasu jarumai fitattu da suka samu daukaka a fagen fim din Hausa kamar Ali Nuhu da Adam A Zango, sai dai rashin jituwar da mutanen biyu ke yi ta sa ana nuna shakku kan wayewarsu da fargaba kan makomar masana'antar, wacce ke fama da karancin shugabanci nagari.
Ba dai yanzu ne jaruman biyu suka fara samun sabani ba, kuma duk da cewa an yi kokarin sulhun tasu a baya, amma batun na ci gaba da ruruwa.
A 'yan kwanakin nan, kafafen sada zumunta musamman Instagram sun cika da kalaman batanci da habaici, a wasu lokutan ma har da zage-zage da ke kaiwa da komowa tsakanin magoya bayan jaruman biyu.
Duk da cewa duka Ali Nuhu da Adam Zango ba su fito fili sun tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin ba, a zahiri ta ke cewa sun san abubuwan da ke gudana, domin abin ya kai matakin da ba zai yi wu na ce ba su sani ba.
Me ya hada fadan, kuma su waye ke ruruta shi?
Zai yi wuya ka fito ka ce ga abinda ya haddasa wannan rashin jituwar ta baya-bayan nan, amma dai abin da ya fito fili shi ne, akwai wasu da za a iya dora alhakin tabarbarewar lamarin a kansu.
Ba wasu ba ne illa 'yan fada ko kuma masu dabi'ar fadanci. Suna yawo nan da can suna fadar karya da gaskiya domin neman gindin zama a wurin jaruman biyu.
A don haka ya kamata a fallasa masu ruru wutar rikin nan, a kunyata su, sannan a hukunta su idan ba su daina ba. Wasunsu fa ba za su taba son a zauna lafiya ba, ba za su taba son su ga an yi sulhu ba, domin kuwa ba su da kwarewar da za su iya fitowa a babban fim ba, in ba tare da fadanci da banbadanci ba.
Dole ne a kauda dabi'ar nan ta fadanci ga wanda ya kawo jarumi Kannywood, da kuma kokarin kushe abokin hamayyarsa. Hakan na nuna irin raunin harkar fina-finan na Hausa, domin kuwa tana nuna cewa gaba daya masu harkar tunani daya kawai su ke yi, kuma manufarsu ma iri daya ce.
Abu ne mai kyau ka girmama duk wanda ya daura ka a wata hanya, ko ya taimake ka, amma za ka iya hakan ba tare da ka ci mutuncin wasu ba.

Tasirin Ali Nuhu da A Zango a Kannywood

Yanayin zamantakewa a rayuwa da kuma lura da abubuwan da kan faru yau da kullum sun nuna cewa, kishi wata dabi'a ce ta mutane da dabbobi. Zai yi wuya a ce wasu da suka yi tarayya a wani abu guda ba sa kishi da juna.

Ali Nuhu da Adam Zango
Image captionJaruman biyu sun dade suna sharafi a fagen Kannywood

Kishin ya kan yi tsanani idan wani ya yi wa sa'anninsa zarra, hakan zai iya sa wasu su fara yi masa hassada da tunanin mai ya sa wane zai fi ni.
A wasu lokutan ko da mutanen biyu suna zaune lafiya, na kusa da su sai sun kunna wuta tsakaninsu.
A Kannywood, sama da shekara 10 ake dangantaka tsakanin taurari biyu Ali Nuhu da takwaransa Adam A. Zango. Ali Nuhu ya fi Adam Zango shekaru kuma ya riga shi fara fim.
Ko a kwanakin baya, Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa shi ne ya fara saka Adam Zango a fim.
Duk da cewa akwai wasu kwararrun jaruman masu basira, amma dai har yau ba bu kamar wadannan biyun wajen daukaka. Haka rayuwa ta ke.
A yanzu duka jarumai masu tasowa na kokarin bin sawun Ali da Adam, to sai dai abin takaici shi ne matasan biyu sun dau dogon lokaci ba sa ga-maciji.
A duniya, ba ka raba taurari da janyowa kansu magana. Hakan na taimaka musu wajen daukar hankulan kafofin watsa labarai. Kuma yawan ambaton jarumi shi ya ke maida shi shahararre.
A bisa tsarin rayuwa, a kan samu sabani duk lokacin da mutane suka yi mu'amala, ko aiki, ko zama tare. Don haka taurari da dama suna hamayya da juna.

Wannan layi ne

Rayuwar Ali Nuhu a takaice
  • An haife shi a watan Maris na 1974
  • Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin Kano
  • Ya yi digiri a jami'ar Jos, kuma ya yi hidimar kasa a jihar Oyo a 1999
  • Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da Turanci
  • Yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara fitowa a fina-fina Nollywood
  • Ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen Najeriya
  • Ya ci lambobin yabo da dama, abin da ya sa ake masa lakabi da Sarki

Wannan layi ne

Illar da fadan ka iya jawowa Kannywood

Matsalolin da Kannywood ta ke fama da su sun isa haka. Na san cewa wasu za su ce ko a masana'antar fina-finan India ta Bollywood da ta Amurka Hollywood ana samun irin wannan matsala tsakanin manyan taurari.
Haka ne, domin misali kullum ana kasayya tsakanin Amir Khan, Salamn Khan da Sharukh Khan tun shekarun 1990, haka kuma taurari mata da dama suna rigima da dama kan samari, da fitowa a fim, da kyautuka.
To sai dai karan masana'antarsu ta kai tsaiko don haka irin wadannan matsalolin ba za su shafe ta ba.
Masana'antar Kannywood wata karamar masana'anta ce da tun kafuwarta sama da shekara 20, take fama da suka daga mutanen da ke ganin tana gurbata al'adun Hausa da addinin Musulunci.
Bisa la'akari da wannan, a iya cewa duk wata badakala, da gaba, da rashin hadin kai babu abin da za su haifarwa Kannywood din sai koma-baya.

Ali NuhuHakkin mallakar hotoALI NUHU INSTAGRAM
Image captionMagoya bayan Ali Nuhu na kiransa 'sarkin' Kannywood saboda irin tasirin da yake da shi

Sama da shekara 10, har yanzu ana sanya misali da ci gaba da tattaunawa kan hoton bidiyon tsiraici na Maryam Hiyana. Ko irin wannan kadai ya isa a ce ya janyo hadin kai da taka-tsantsan a masana'antar.
A yanzu rashin-jituwa tsakanin Ali Nuhu da Adam Zango kadai ta isa ta gasganta zargin masu cewa su kan masu harkar fina-finan ba su da tarbiyyar da sanin ya kamata da har za su iya koyar da wata kyakkyawar tarbiyya ko fadakar da masu kallonsu, kamar yadda kullum suke ikirari.
Ta fuskar zamantakewa da sanin ya kamata, abin kunya ne yadda mabiyan taurarin biyu suke musayar mugayen kalamai, da habaici, wasu lokutan ma har da zage-zage.
Ba makawa, wannan na nuni da irin dabi'a da tarbiyyar masu fina-finan na Hausa tun daga kan mutanen biyu.
Saboda dimbin magoya bayan da suke da shi, rikicin ya kusa raba kan masana'antar ta Kannywood gida biyu. Hakan ta sa har a kan samu wasu taurari suna sauya sheka daga wannan bangare zuwa wanda suka ga za su fi samun biyan bukata.
Kazalika hakan ya sa a wasu lokutan a ke kin saka wasu taurari a fim saboda ana ganinsu a matsayin 'yan gidan abokan gaba.
Kuma shi ya sa a wasu lokutan a kan sa wadanda ba su dace ba su taka wata rawa a wasu fina-finan, wanda kuma hakan koma-baya ne.

Wannan layi ne

Rayuwar Adam A Zano a takaice
  • An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
  • Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
  • Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
  • Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan lokacin
  • Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa
  • Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
  • Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
  • Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara 16

Wannan layi ne

'Ko a gidan giya akwai babba'

Yawan magoya baya da makiya da suke da shi ya kuma sa duk abinda suka yi yana jawowa Kannywood din bakin jini ko akasin haka.
Akwai ma wasu karin wasu illolin da rikicin ya ke yi wa Kannywood. Ba manufatace in ce wane ne da laifi ko wane ne da gaskiya ba.

Adam ZangoHakkin mallakar hotoADAM ZANGO INSTAGRAM
Image captionAdam A Zango yana dimbin magoya baya a ciki da wajen Najeriya

Amma dai ana cewa ko a ginda giya akwai babba. Don haka ya kamata Adam Zango ya ja kunnen magoya bayansa da suke ganin dai-dai ne cin mutuncin Ali Nuhu.
Shi ma a nasa bangaren, ya kamata Ali Nuhu ya gane cewa sun jima tare da Adam Zango suna abota da ya kamata ma a ce sun zama 'yan uwa. Don haka shi ma ya kamata ya magantu ya gargadi magoya bayansa.
Dole ne duka su biyun su gargadi magoya bayansu cewa duk wanda ya kara zagin wani to sun raba-gari.

'Babu shugabanci nagari'

Kungiyar masu fina-finai da manyan cikinsu ya kamata su ma su tsara kansu, su zama suna damuwa da abinda ke faruwa a Kannywood, su samarwa kansu kima da za su iya jan kunnen duk wanda yake kokarin raba kan 'ya'yan 
masana'antar.
Abin takaici ne ganin yadda ba a je ko ina ba, aka koma ruwa bayan sulhun da darakta Falalu Dorayi ya shirya, kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Isma'ila Na'abba Afakallah ya jagoranta.
Mai yuwa hakan ba zai rasa nasaba da rashin fayyace hukunci kan duk wanda aka samu da laifin saba ka'idojin sulhun ba.
Don haka dole ne kowa ya shigo a samu domin daidata manyan taurarin. Domin kuwa masana'antar ta fi kowa daga cikin su biyun muhimmanci, don haka ya kamata a tsawatar musu.

Source BBCHausa.Com

Post a Comment

0 Comments