Menene Gaskiyar Lamari Game Da Karbar Musuluncin Solomon Dalung?

- Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya kai ziyara wajen tafsir 
- Sheikh Pantami ya yi masa maraba da zuwa tare da nasiha irin ta su ta Malamai 
- Ya yi kira ga Solomon Dalung da yayi Imani da Annabi Muhammad S.A.W, ya shiga Addinin Musulunci Barrista Solomon Dalung, ministan matasa da wasanni, yakai ziyara wajen tafsir na Sheikh Dr Isa Ali Pantami da ya gabatarwa a Masallacin Anur-Mosque, Wuse II, Abuja a ranar Alhamis.

Sheikh Pantami ya yi masa maraba da zuwa tare da nasiha irin ta su ta Malamai da kira ga shi Solomon Dalung da yayi Imani da Annabi Muhammad S.A.W, ya shiga Addinin Musulunci. 


A jawabin sa Barrista Dalung yace ya samu goron gayyata da Malam Pantami yayi masa kuma zai yi Tunani Akai. 

Domin haka Barrista Solomon Dalung bai karbi Musulunci ba a wajen Tafsir na Malam 

Post a Comment

0 Comments