Mutane 12 Da Ka Iya Maye Gurbin Buhari A Zaben 2019



Kamar a jiya ko shekaranjiya ne aka rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya kayar da shugaban kasa na wancan lokaci, Goodluck Ebele Jonathan. Amma za a iya cewa kusan shekara biyu kenan, tun bayan nasarar da jam’iyyar adawa ta APC ta samu a kan jam’iyya mai mulki PDP a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a cikin watan Maris, 2015.
Ba a zaben shugaban kasa kadai PDP ta sha mummunan kaye ba, har ma da zaben gwamnoni, inda a Arewa ta tsira da jihohi biyu tal, da yarfe gumin goshi, wato jihohin Gombe da Taraba.
Ganin cewa an ci rabin zangon wa’adin shekara hudu, Ashafa Murnai da Muhammed Lere na PREMIUM TIMES HAUSA ne suka yi cikakken nazarin abin da ka iya biyo baya a zaben 2019 mai zuwa domin yin hasashen angon da Najeriya za ta sake aura a cikin wasu zawarawan ta goma.
Saura shekara biyu kenan za a iya cewa a sake rantsar da wani shugaban kasa, imma dai a nanata rantsar da mai ci a yanzu, Shugaba Muhammadu Buhari, ko kuma idan jam’iyyar adawa, PDP na da karfin sa kwace mulki, to sai a rantsar da dan adawa kenan. Wato dan adawa Buhari ya hau, kuma dan adawa zai kowace.
Sai dai me? A cikin masu adawa, ko akwai wanda zai iya gogawa da Shugaba Buhari har ya kayar da shi? Shin PDP ta fara shirin karbar mulki tun yanzu ganin yadda laimar PDP ta kama da wuta, kuma har yau an kasa yin gangamin kashe wutar?
Wata tambayar kuma ita ce, ko Buhari zai sake tsayawa takara, ganin yadda mutane da dama ke lura da cewa yayin da lokaci ke kara ja, kamar kuzarin sa na raguwa? Idan zai sake tsayawa, wa zai iya ja da shi? Idan ba zai sake tsayawa ba, wa zai yarda da shi ya tsaya a matsayin dan takarar APC.
Tashin farko dai ya kamata mai karatu ya san cewa dukkan ‘yan takarar PDP da na APC duk daga Arewa za su fito.
Jam’iyyar APC:
1. MUHAMMADU BUHARI:
President-Muhammadu-Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne da kamar babu irinsa a yankin Arewacin Najeriya yanzu. Sau dayawa masu nazarin siyasa kan ce bayan Marigayi Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, babu wani dan Arewa da ya ke da farin jinin da Buhari ya samu yankin.
Duk da cewa sunan sa a fagen siyasar Najeriya ba boyayyiya bace domin tun a Shekarar 2003 ya fara fitowa takaran sake zama shugaban kasa amma Allah bai sa hakan ya yiwu ba sai a 2015, wanda itace karo na hudu da yake fitowa takara.
Buhari zai iya maye gurbin Buhari idan aka yi la’akari da abubuwa da dama. Na farko dai har yau bai fito ya ce ba zai iya sake tsayawa takara ba. Na biyu kuma ‘ya’yan jam’iyyar APC manya da kanana za su so a ce shi ne ya kara tsayawa, domin da dama saboda albarkacin sa ne aka ci zabe, dalilin furucin sa na cewa a yi “sak” a lokacin zaben 2015.
Don haka idan ba Buhari ba ne, zai yi wahala talakawan da suka saida ran su saboda Buhari, su sake irin dukan jikin su da danyen kara kamar yadda suka yi a 2015.
Irin yadda a yanzu ake ta bankado asirin wadanda suka wawuri dukiya a lokacin gwamnatin Jonathan, hakan na kara kashe kaifin PDP sosai, baya ha cewa rigingimun cikin gida na shuhabanci ya dabaibaye jam’iyyar.
Duk da ana cikin kukan matsin fatara da kuma talauci, wannan bai kashe kaifin kaunar da ake yi wa Buhari ba. Da yawa na kallon cewa gwamnatin Jonathan ce ta jefa kasar nan cikin halin-kaka-ni-ka-yi, duk kuwa da cewa ba a irin wahalar da ake sha yanzu a lokacin gwamnatin Jonathan ba.
Akwai wata waina ba ta wake ba. Ana lura da cewa kuzarin Shugaban Kasa ya na raguwa kwarai tun bayan dawowar sa daga ganin likita a London, inda ya shafe sama da wata daya. Kafin nan, Buhari ya rika yawan kai ziyarce-ziyarce kasashe da dama, har ta kai an fara kokawa da yawan tafiye-tafiyen sa, ‘yan adawa sun fara ce masa “Baba Yawale.”
Amma tun bayan dawowar sa daga ganin likita, an daina ganin kazar-kazar din sa a sha’anin gudanar da ayyuka da dama. Ya rika wakilta Mataimakin sa Osinbajo zuwa wasu wurare ko wani aiki na musamman.
Idan ta kasance an ba shi shawara ko ya yanke wa kan sa hukuncin ba zai sake tsayawa takara ba, duba da wadancan dalilai na sama da kuma yanayi na yawan shekaru, to wa APC za ta tsayar matsayin dan takarar Shugaban Kasa?
2. ATIKU ABUBAKAR:
Atiku-Abubakar
Ko shakka babu, Atiku Abubakar ya na son zama shugaban kasa, idan aka yi la’akari da cewa ya taba yin takara har sau uku baya. Ya yi a 2007 karkashin jam’iyyar ACN, a 2011 ya fadi a zaben fidda-gwani na PDP, a 2015 kuma ya fadi a zaben-fidda-gwanin APC.
Babu ko tantama Atiku mutum ne mai karfin siyasa da kuma karfin arziki. Cikakken dan kasuwa ne wanda karfin Dangote ne ya dusashe karfin arzikin sa a Nijeriya, shi ya sa ba a saka shi cikin manyan attajirai. Watakila saboda kallon da ake masa na dan siyasa.
Atiku dan asalin gidan siyasar Shehu Musa Yar’Adua ne, kamar yadda shi ma ya sha furtawa.
Bayan ya ci zaben 1999 ne a matsayin gwamnan Jihar Adamawa, sai kuma aka tsaida shi mataimakin dan takarar shugaban kasa na lokacin a karkashin jam’iyyar PDP, wato Olusegun Obasanjo, inda ya yi shekara takwas a matsayin mataimaki.
Ya tsaya takarar shugaban kasa a 2007 karkashin CAN, a 2011 kuma yay i takarar fidda gwani a PDP, yayin da a 2015 kuma yay i takarar fidda gwani a APC.
Kada a manta, Atiku ne silar karya lagon PDP a kasar nan, yayin da ya jagoranci zugar hwamnoni bakwai suka fice daga taron PDP a dakin taro na Yar’Adua Center a Abuja. Hakan ta sa suka balle suka hadu da ACN, ANPC, APGA da CPC suka APC wacce ta kayar da PDP a zaben 2015.
Ko da jam’iyyar APC ba ta fitar da kudi an yi bushasha a zaben 2019, tsayar da Atiku zai iya yin bakin-rai-bakin-fama wajen yin amfani da kudin sa domin ya ci ZABEN a takarar da zai ga kamar ita ce damar sa ta karshe.
Kasaitaccen attajirai Atiku, a wata hira da na yi da shi cikin 2013, ya bayyana min cewa duk wani katin waya na MTN ko Glo ko Etisalat da Airtel, duk kamfanin sa ne ke buga wa kamfanin shaida layukan wadannan katittika.
Ya kuma ce min a duk wata ya na kashe sama da naira milyan 350 a jami’ar APTI-American University da ke Yola. Ya jaddada cewa akwai ma’aikatan da ke karbar albashi kusan dubu 50 a karkashin kamfanonin sa daban-daban da suka hada har da ruwan Faro da kamfanin yin abincin dabbobi da sauran su da dama.
Ko a zaben 2011 bayan Jonathan ya kayar da Atiku, sai da Atiku ya taimaka wa Buhari da gudummawar naira milyan 400. Haka ya shaida min a waccan hira da na yi da shi.
Matsalar Atiku ba ta wuce kallon da ake yi masa a matsayin daya daga cikin shugabannin da suka ci moriyar gwamnati ba. Sai dai har zuwa yau ba a taba samun sa da laifin da aka maka shi kotu ba, balle ma a ce ko EFCC sun taba kai samame gidan sa.
Atiku mutum ne mai saukin kai, kuma mai jimirin iya yakin siyasa. Lokacin da tsohon Shugaban Kasa Olisegun Obasanjo ya nemi hana shi tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2007, sau shi da ya na kayar da Obasanjo a kotu. Wani abin da ba a sani ba dangane da Atiku, ya shaida min cewa tun da ya fara aikin kwastam har ya zama Shugaba Kwastan na Kasa, bai taba kowace kayan kowa ba.
3. RABIU MUSA KWANKWASO:
kwankwanso-NEW
Idan ana maganar gwarzon iya kokawar siyasa, tilas a saka tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a sahun gaba. Ya kasance shi da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi ne suka fi shigewa hancin Shugaba Goodluck Jonathan, kuma ya kasa fyace su, har sai da suka hada masa jibi da majina.
Kwankwaso tsohon dan siyasa ne, ya taba rike mataimakin shugaban majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar SDP. Shi ne ya yi gwamnan Kano a 1999 zuwa 2003 a karkashin jam’iyyar PDP. Sai dai ya na kan mulki abokin takarar san a jam’iyyar ANPP, Malam Ibrahim Shekarau ya kayar da shi a zaben 2003.
Daga nan, shugaban kasa na lokacin, Olusegun Obasanjo ya nada shi Ministan Tsaro. Karfin siyasar Kwankwaso ya kara tasiri a 2011, yayin da ya sake tsayawa takarar gwamnan Kano, inda ya kayar da dan takarar ANPP, Salihu Sagir Takai, wanda ya tsaya wa jam’iyyyar bayan da Shekarau ya kammala wa’adin san a shekara takwas.
Matasan Arewa na son salon siyasar Kwankwaso ha cika-baki, hayagaga da kuma rashin tsoron wajen firzas da duk abin da ke cikin bakin sa ko wanda ya ga damar firzas wa idan yah au duro. Tamkar dai salon siyasar marigayi tsohon gwamnan Kano, Alhaji Abubakar Rimi.
“ Ma’anar tutar PDP it ace kore ya na nufin yalwar arziki, fari kuma na nufin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ma’anar ja kuwa, ja danjaros kenan yaro in b aka sani ba gar aka sani. Mu ne maganin maaahaha, maganin wannan ja danjaros yaro in ba ka sani ba, gara ka sani. In ba haka ba, ko a sa maka jambaki, ko a sa ka ci goro dan Ujile, ko kuma, yaro ka ji wuji-wuji ka zaga, dole abin da ka zo ka yi ka hakura. 2011 ba za ka yi zabe ba, an yi zabe an gama, Rabi’u Kwankwaso ya ci zabe a ba shi tuta!’”
Arewa kusan shi ne ya fi karfin magoya bayan siyasa a cikin jam’iyyar APC, idan ka fidda Buhari. Ko a zaben fidda-gwani na 2015, shi ne ya zo na biyu bayan Buhari. Kwankwaso ne Sanatan da ya fi kowane Sanata yawan ruwan kuri’u a duk dadin kasar nan. Sannan kuma shi ne gwamnan da jihar sa ta fi jefa wa Buhari ruwan kuri’u a zaben Shugaban Kasa.
Allah ya yi masa farin jinin matasa, kuma mutum ne wanda ya iya takun siyasa matuka. Ko shakka babu idan APC ta tsaida Kwankwaso, to matasa za su ce na su ya samu, sai inda karfin su ya kare. Dama kuma yawancin matasa ‘yan-a-mutun-Buhari musamman a Kano, duk gyauron siyasar Kwankwasiyya ne.
Kwankwaso ba zai samu matsala sosai ba, domin a na ganin a duk kasar nan ba ya shakkar komai kuma ba ya tsoron kowa. Ana yi masa kallon mutumin da zai iya karfafa hukumar EFCC a matsayin ta na karen-kamun-masu-laifi.
4. NASIRU EL-RUFA’I:
elrufai (1)
Gwamnan Jihar Kaduna na yanzu Nasir El-Rufai ya na da damar maye gurbin Buhari idan har aka tsaida shi takara. El-Rufai wukar yanka giwa ce, wadda ba girma ake bukata ba, sai kaifin ta. Shi ne mutum na farko da ya fara aikin gyara na ba-sani-ba sabo a Abuja lokacin ya na Minista na Babban Birnin Tarayya. Mutum ne kuma mai kokarin bin tsarin doka ba dan-ta-ci-barkatai ba ne.
Duk da cewa bai dade da shiga siyasa sosai ba, El-Rufai ya shige ta a sa’a, inda a lokacin murkin Obasanjo, aka dauko shi daga hukumar saida hannayen jarin gwamnati ta kasa, aka nada shi minIstan Abuja. Bayan ya sauka daga minista, ya bar kasar nan na dan wani lokaci a zamanin mulkin Ummaru Musa ‘Yar’Adua, inda ya dawo bayan da Jonathan ya hau mulki.
El-Rufai ya shiga jam’iyyar CPC, ya hade tare da buhari, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen dunkulewar jam’iyyun adawa wuri daya, domin samun karfin da kayar da PDP.
Da yake El-Rufai ba sanannen dan siyasa bane kafin 2015, mutane da yawa suna masa ganin shi ma’aikaci ne amma mua’mula da mutane zai yi masa wuya wanda kuma shine siyasa ta gada.
Farin jinin sa a siyasance ta samu asaline dalilin shakuwarsa da Buhari kuma hakanne ya sa mutane da yawa ke masa ganin har idan Buhari ba zai yi takara ba, to El-Rufai zai mika wa kambun.
Wani babban abu da zai iya zama masa matsala idan har zai fito takara shine, rashin jituwa da manyan ‘yan siyasa da wasu jiga-jigan jam’iyyar musamman a jiharsa ta Kaduna da na kasa in da yanzu haka jam’iyyar APC ta rabu kashi biyu a jihar Kaduna.
5. NUHU RIBADU:
Ribadu Nuhu
Idan ta yi wani juyin har aka ba Nuhu Ribadu takara, to zai iya maye gurbin Buhari. A matsayin sa na Shugaban EFCC, ya kasance bai tsohon kama kowa a kasar nan. Har Ogan sa Tafa Balogun sai da ya sa wa ankwa. Mutum ne wanda bai yarda da cin hanci ba, kuma ya sha nanatawa cewa tun da ya ke bai taba karbar cin hanci ba, idan akwai mai shaida to ya fito ya karyata shi. Ribadu na da goyon baya har a Kudancin kasar nan. Matsalar sa kawai ficewar da ya yi daga APC ya koma PDP a 2015 inda ya yi takara a jihar Adamawa. Wannan ma ba a kira ta babbar matsala, tunda a yanzu ya dawo APC.
Duk da cewa a yanzu dai ba boyayye bane a fagen siaysar Najeriya domin yana daya daga cikin wadanda suka fafata a 2011 lokacin da ya fito takaran shugabancin kasa Najeriya a jam’iyyar ACN.
Nuhu na daga cikin wadanda suka sami goyon bayan matasa a wancan lokaci fiye da kowani dan takara amma duk da hakan bata haifar da da mai ido ba.
6. BUKOLA SARAKI:
Saraki-3ar tayi karfin da ko shugaban kasa a wancan lokacin sai ya nemi shawarar gwamnoni kafin ya aiwatar da wasu ayyuka.
Bukola yana daya daga cikin wadanda sukayi ruwa sukayi tsaki don ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a 2015.
Shine shugaban Majalisar dattijai kuma iya siyasar sa ta sa ya samu karfin da yadda yake so a majalisar haka akeyi.
Babban Matsalar da Bukola zai iya samu a zaben da ke tafe idan har zai yi takarar shugaban kasa shine laifukkan cin hanci da rashwa da handame kudaden gwamnati da ake zarginsa da yi wanda har yanzu yana fuskantar shari’a a kotun kula da da’ar ma’aikata, CCT.
Jam’iyyar PDP:
7: SULE LAMIDO:
Sule Lamido
A siyasance, kuma a Arewacin Najeriya tsohon Gwamnan Jihar,Jigawa, Sule Lamido shi ne ya fi kowa gogewa da kuma gogayya a yanzu a cikin jam’iyyar PDP, har ma da APC din ita kan ta. Tashin farko da mutum ne mai ra’ayin akidar kawo sauyi. Irin mutanen nan ne da kan dauki siyasa bakin-rai-bakin-fama. Ba kasala kuma ba gajiya.
Duk wani abin da ake ci ko ake sha na riba ko wahalar siyasa, to Sule Lamido ya ci kuma ya sha. Sunan sa ba zai taba kankaruwa ba a matsayin daya daga cijin kungiyar G9 ko G10 da suka rika yakin fatattakar sojoji daga kan mulki da nufin dawo da dimokradiyya cikin 1998. Ya sha rana ya sha dauri, ya sha tsangwama, amma bai fasa ba, bai gaza ba. Karewa-da-karau, da shi ne aka kafa jam’iyyar PDP, domin su ne suka kara wa G9 yawa ta kai G18 har ta nausa ta kai G38.
Tsohon dan jam’iyyar PRP ne, wanda ba ya tsoron fadin abin da ke zuciyar sa.
Lokacin ya na Ministan Harkokin waje a zamanin mulkin Obasanjo, Sule Lamido ya taka rawa wajen dawo da, martabar Najeriya a idon duniya,sannan ya yi rawar gani wajen yafe wa Nijeriya wasu basussuka a lokacin ya na Minista.
A shekara takwas da ya yi ya na gwamnan Jigawa, ya,yi ayyuka da daman a raya kasa da ya sami yabo daga mutanen jihar.
Ya na daya daga cikin ‘yan siyasar da suka kafa PDP tare da abokin siyasar sa Marigayi Abubakar Rimi da irin su Cif Solomon Lar. Magoya bayan Sule Lamido, musamman Alhaji Aminu Ringim, wanda ya yi takarar gwamnan Jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2015, su na ganin cewa jam’iyyar APC ta cika duk wasu sharudda na faduwa zabe. Don haka Sule Lamido ne kawai zai iya kawo gyara a Najeriya.
Babbar matsalar Sule Lamido ita ce rikicin shugabanni na.
8. ALI MODU SHERIFF:
Ali Sharreef
Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon Sanata ne kuma tsohon gwamnan Jihar Barno daga tsohuwar jam’iyyar APP. Daga baya ya koma jam’iyyar PDP. Ya na da karfin siyasa matuka, sai kuma ganin yadda shigar sa jam’iyyar PDP ta haifar da rudu, hakan ya rage masa wani tasiri kuma ya dusashe hasken tauraron sa.
Masu nazarin siyasa sun ce tatsuniyar siyasa da rikicin shugabancin jam’iyya wanda Sheriff ke yi da Sanata Ahmed Makarfi, duk fada ne na share fagen tsayawa takarar shugabanci a zaben 2019.
Sheriff zai yi bakin kokarin sa wajen ganin ya samu tikitin tsayawa takara, kuma da PDP za ta mara masa baya, to zai yi kokari matuka. Amma ganin yadda yawancin gwamnonin PDP a Kudancin kasar nan, irin su Gwamna Wike na Jihar Ribas da Ayo Fayose na Ekiti duk ba su tare da Sheriff, hakan alama ce mai nuna cewa da wuya hakar sa ta cimma ruwa.
Danganta Sheriff da ake yi da cewa shi ne gwamnan da ya yi sakaci har Boko Haram ta bayyana, hakan na karya masa lagon siyasa. Har ta kaia wasu na,yi masa zargin ya na daya daga cikin iyayen gidan kungiyar, zargin da ya sha fitowa a kafafen yada labarai ya na karyatawa.
9. AHMED MAKARFI:
Makarfi
Sanata Ahmed Makarfi na daya daga cikin wadanda ake ganin suna son tsayawa takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP. Ana ganin dalili kenan ya tsaya ya ke ta tafka rikicin shugabanci tsakanin sa da Sanata Sheriff. Makarfi tsohon gwamna ne a jihar Kaduna tsakanin 1999 zuwa 2007.
Ya kasance a zamanin sa rikice-rikicen addini da na siyasa sun dabaibaye jihar. Sai dai namijin kokarin da ya yi wajen shawo kai da magance kashe-kashe a cikin Kaduna sun janyo masa farin jibi sosai, musamman yadda ya rika kakkafa kananan sansanonin sojojin kar-ta-kwana a unguwannin da ake ganin daga can ne ake cunna wutar fitintinu.
Zai iya samun goyon bayan ‘yan jam’iyyar.
10. IBRAHIM SHEKARAU:
shekarau
Tsohon Gwamna a Jihar Kano daga 2003 zuwa 2011, Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar ANPP ya koma PDP tun bayan da Kwankwaso ya koma APC. Hakan ta faru ne ganin cewa a lokacin Kwankwaso ne gwamna, wato jagorancin jam’iyya ya koma a hannun babban abokin adawar sa.
Shekarau ya koma PDP da kafar dama, domin Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ba shi mukamin Minista Ilmi. Ya na da magoya baya sosai, kuma ya iya siyasa. Sai dai kuma rashin saurin kakkafa jama’a da neman magoya baya, su ne matsalar sa.
11. IBRAHIM DANKWAMBO:
Dankwambo 3
Ibrahim Dankwambo ba zai ta da hankalin ‘yan siyasa ba musamman ‘yan jam’iyyar PDP saboda kusan shine wanda bai taba wuce mukamin gwamna ba a siyasance cikin wadanda ake sa ran za su goge raini idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai yi takara ba.
Ko da yake ya nuna bajintarsa a zaben 2015 inda ya ja da Danjuma Goje kuma ya kasa dan takaran jam’iyyar APC a jihar duk da goguwar Buhari da ta mamaye duk Arewa a wancan lokacin.
Ibrahim Dankwambo yana da burin ya fi haka bayan ya kammala wa’adinsa na gwamnan a jihar Gombe. Shima zai fito da tasa salon idan har ya zai bidi kujeran shugabancin Kasa Najeriya.
12. DAVID MARK:
Mark david
Tsohon shugaban majalisar dattijai David Mark na daya daga cikin ‘yan arewan da zasu iya zama shugaban kasa a Najeriya.
Koda yake ba shahararren dan siyasa bane idan har za a yi gwaji a tsakanin wadanda zasu iya fitowa a jam’iyyarsa ta PDP, David Mark kwararrene ne kuma shahararren dan majalisa ne kuma yana da saukin kai da iya jagorantar mutane.
Gashi tsohon soja kuma attajiri, har yanzu yana da karfin gaske a siyasar jiharsa ta Benue da kuma ta kasa.

Source : Premium Time

Post a Comment

0 Comments