Yanda Ake Gyara Memory Card Ko Flash DinKa Idan Ya Lalace Yayi





Memory Card
 Shine Abu Na Biyu Mafi Soyuwa Da Muhimmanci A Cikin Waya Bayan Sim Card,

MukanJi Ba Dadi Yayin Da Memory Card Dinmu Ya Lalace (Currupted)

Misali Kana Kan Amfani Da Memory Card DinKa, Kwatsam Sai Kaga Ya Nunama "Damaged SD Card"InKayi Format Din A Cikin Wayar Yakiyi, Inma Ansa A Computer Anyi Format Dinsa Haka Zai Ta Nuna Maka Koda Kayi Format Din Bazai Ci Gaba Da Amfaniba Kuma ...


A Takaice Dai Memory Card DinKa Ya Lalace Ka Rasa Komai Na Cikinsa, Ka Rasa Shi Kansa Memory Card Din

Abin Da Zamuyi Magana A Yau Shine Yanda Zaka Gyara Memory Card DinKa A SauKake Ba Tare Da Kayi Amfani Da Wani Software Ba .....

Abubuwan Da Ake BuKata Kafin Gyara Memory Card Ko Flash,...

1, Natsuwa .. Yana Dakyau Ka Natsu Sosai WaJen Gyara Lalataccen Memory Card Ko Flash DinKa,

2, Lalataccen Memory Card, Tare Da Card Reader, Waton Gidan Sa Memory Card Din

3, Computer, Dole Da Ita ZaKayi Aikin WaJen Gyara Memory Card Din NaKa .

Da FarKo Ka Bude Coputer Din SaiKa Danna Alamar Windows Din Computer Din,



Zai Fitoma Da ShafuKan Computer Din A Kasa Akwai WaJen Search Sai Ka Rubuta "CMD" Kana Ruburawa Zakaga Ya Fito, SaiKa Budeshi

Inya Bude SaiKa Rubuta DISKPART SaiKa Taba Enter Key Na Computer Din

Daganan Zai KaiKa Wani Shafin, Sai Ka Rubuta “LIST DISK SaiKa Danna Enter Key

Zai Nunoma DisK Wato Memory Din Computer Din Da Kuma Lalataccen Da Kasa ... Sai Ka Duba Kaga Wannene Lalataccen A Ciki, Disk 1 Ne Ko DisK 2, Amma Yawanci Yafi Zuwa A DisK 1,

Sai Ka Rubuta “SELECT DISK 1” Sai Ka Taba Enter Key

Zai Nunama

DISKPART> DisK 1 Is Now Selected

Sai Ka Sake Rubuta “CLEAN” SaiKa Taba Enter Key

DisKPart> Succeed Cleaning The Disk.

Saika Sake Rubuta “CREATE PARTITION PRIMARY” Sai Ka Taba Enter Key, Zai Nunoma

DISKPART> Succeed Creating In The Specified Partition

Sai Ka Rubuta “ACTIVE”

SaiKa Taba Enter Key

Zai Nunoma

DISKPART> Marked The Current Partition As Active

SaiKa Rubuta “SELECT PARTITION 1” SaiKa Taba Enter Key

Zai Nunama, Partition 1 Is Now The Selected Partition

Sai Ka Sake Rubuta “FORMAT FS=FAT32” SaiKa Taba Enter Key

Daganan Zai Fara Format Zakaga Yasama 0% To Complete, A Haka A HanKali Har Sai YaKai 100 %

Ka Tabbatar Kayishi Kamar Yanda Yake A Wannan Hoto




YaKan Dau Lokaci Kafin Ya Gama Gyaruwa

Post a Comment

0 Comments